17 Yuli 2026 - 11:14
Source: ABNA24
Iran: Ta Kai Hari Kan Cibiyar Umarni Ayyukan Amurka A Siriya

Dakarun Juyin Musulunci na Iran a cikin wata sanarwa sun ba da rahoton harin bazata da suka kai a kan cibiyar kwamandancin ayyuka na musamman na makiya a yankin Al-Tanf na Siriya, a matsayin ramuwa ga jinin sojojin shahidan Iran shahr.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Ofishin Hulda da Jama'a na Dakarun Juyin Musulunci na Iran a cikin sanarwa mai lamba 19 na aikin Nasr 2, da lambar sirri mai albarka ta "Ya Aba Abdillahil Husain (A.S)," sun kawo cewa:

A martani ga munanan ayyukan sojojin Amurka makisa yara, mayakan rundunar sararin samaniya na dakarun juyin musulunci, a zagaye na goma sha ɗaya na aikin Nasr 2, da lambar sirri mai albarka ta "Ya Aba Abdillahil-Husain (A.S sun kai harin bazata a kan cibiyar kwamandancin ayyuka na musamman na makiya a yankin Al-Tanf na Siriya, baya ga lalata wata na'urar radar, da jirage masu saukar ungulu na ayyuka na musamman, a matsayin ramuwa ga jinin sojojin shahidan na daren jiya a Iran shahr, dimbin sojojin Amurka masu laifi suka sheka a harin.

Sun kara da cew: Cikakken ikon sarrafa mashigar Hurmuz har yanzu yana hannun jaruman mayakanmu, kuma matuƙar munanan ayyukan Amurka suka ci gaba, ba za a fitar da ko digo ɗaya na man fetur da iskar gas daga wannan yanki ba

Kuma Babu Wata Nasara Fa Ce Daga Wurin Allah Mabuwayi Mai Hikima.

………………………

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha